Edward Akufo-Addo

Me ka ke nema?


Shafin Farko

Edward Akufo-Addo



(Dr.)Edward Akufo-Addo
Hoto: Public Records And Archive Department, Ghana

Gabatarwa

Marigayi Edward Akufo-Addo lauya ne, ɗansiyasa, ɗankishin ƙasa sannan kuma ɗaya daga cikin Turaku Shidan (The Big-Six) Ghana.

Jagoran Jama’iyyar UGCC na farko, Alƙalin Alƙalan Ƙasar Ghana na uku daga ƙarshe kuma zaɓaɓɓen shugaban Ƙasar Ghana na biyu kuma mahaifin shugaban Ƙasar Ghana mai ci yanzu; Nana Addo Dankwa Akufo-Addo. Wannan shi ne mutumin da wannan rubutu ya ƙudurci aniyar damƙa maka shi a hannunka. Amma fa a rubuce.

Haihuwa

An haifi Edward Akufo-Addo a ranar 26 ga watan Afirilun shekarar 1906 a Akropong-Akwapim a wata majiyar kuma aka ce a garin a Dodowa da ke cikin Yankin Babbar Accra (Greater Accra Region) tare da tabbatar da zamowar mahaifansa duka biyu ‘yan asalin Akropong.

Sunan mahaifinsa William Martin Addo-Dankwa. Maihaifiyarsa kuma ita ce Theodora Amuafi.

Karatu

Edward Akufo-Addo ya yi karatu tiryan-tiryan tun daga matakin farko har zuwa digiri. Ya halarci makarantun da suka haɗa da:

  1. Presbyterian Primary and Middle School Akropong.
  2. Presbyterian Training College Akropong.
  3. Abetifi Theological Training College.
  4. Achimota College, 1929.
  5. Karatun Digiri a fannin Lissafi, Siyasa da Falsafa (Mathematics, Politics and Philosophy) a St Peter’s College Oxford 1933.
  6. Horon Lauyanci a Middle Temple, Londo UK, 1940.

Siyasa

Edward Akufo-Addo su suka yanke wa siyasar Ghana cibiya. A cikin shekarar 1947 suka kafa ƙungiyar siyasa mai suna United Gold Coast Convention (UGCC) tare da zamowar gidansa matsugunni ko cibiyar wannan jama’iyya wadda ta zama tubalin ‘yancin kan Ghana da ma Afirka baki ɗaya.

A cikin shekarar 1948 wannan fafutikar samawa Ƙasar Ghana ‘yanci ta kai shi da sauran abokan tafiyarsa shiga gidan-kaso.

Gogayyar Aiki

  1. 1941: Ya fara aikin lauya a matsayin lauya mai zaman kansa.
  2. 1949 – 1950: Ya zama mamba a Majalisar Gudanarwar Yankin Zinariya (Gold Coast).
  3. 1962 – 1964: Ya zama alƙali a Kotun Ƙoli ta Ƙasar Ghana.
  4. 1966 – 1970: Ya riƙe muƙamin Alƙalin Alƙalai ko a ce Babban Maishari’a (Chief Justice) na Ƙasar Ghana.
  5. 1966 – 1968: Shugaban Hukumar Kundin Tsarin Mulkin (Constitutional Commission) Ghana.
  6. 1966 – 1968: Jagoran Jama’iyyar NLC ɓangaren Siyasa.


Fuskokin Turaku Shidan Ghana a Jikin Kuɗin Ghana
Hoto:Babban Bankin Ghana

Shugaban Ƙasa

Edward Akufo-Addo ya samu zama shugana Ƙasar Ghana a ranar 31 ga watan Agustan shekarar 1970 biyowa bayan rantsuwar kama aiki da ya yi a wannan rana.

Sai dai, wannan shugabanci nasa maras cikakken iko ne kasantuwar a wancan salo da kuma tsarin gwamnatin Ghana shi ne cewa dukkan iko ya hannun Firimiya.

Auratayya

Edward Akufo Addo ya auri mata ɗaya mai suna Adeline Yeboakwa Akufo-Addo wadda suka haifi ‘ya’ya huɗu tare da ita. Daga cikin ‘ya’yan nasu akwai wanda yake murza sitiyarin Ghana a yanzu, wato Nana Addo Dankwa Akufo-Addo.

Lambobi Yabo

Kafin rasuwarsa ya karɓi kyutar Digirin-Digirgir daga Jami’ar Oxofrd a shekarar 1971.

Rasuwa

Edward Akufo-Addo ya rasu a ranar 17 ga watan Afirilu na shekarar 1972 biyowa bayan rashin lafiya da ya yi ta fama da ita.

Manazarta

Ghana Web (2021). Edward Akufo-Addo. An ciro a 2021 daga shafin: https://www.ghanaweb.com/person/Edward-Akufo-Addo-123

Modern Ghana (2006). Edward Akuffo-Addo. An ciro a 2021 daga shafin: https://www.modernghana.com/references/34/edward-akuffo-addo.html

Public Records And Archive Department (2019). Edward Akufo Addo. An ciro a 2021 daga shafin: https://praad.goɓ.gh/indeɗ.php/edward-akufo-addo/

Wikipedia (2021). Edward Akufo-Addo. An ciro a shekarar 2021 daga shafin: https://en.wikipedia.org/wiki/Edward_Akufo-Addo


Shafin Tarihi
Shafin Ghana
Ƙabilun Ghana
Yankuna Ghana

Shugabannin Ƙasa


Tarihin Ghana

Haƙƙoƙin 'Yanƙasa

‘Yanƙasanci

Haƙƙoƙi da ‘Yanci

‘Yancin Rayuwa

'Yancin Walwala


Tura wannan shafi zuwa ga abokai ta:


Latsa madannin "Like" ka nuna goyon baya ko kuma "Share" ka yaɗa shafin



Sauran Shafukanmu:

Rumbun Ilimi   Maidarasu    Balangada    Tashar Yutub